Obasanjo ya yabi wani gwamna, ya bukaci ragowar gwamnoni su yi koyi da shi

Obasanjo ya yabi wani gwamna, ya bukaci ragowar gwamnoni su yi koyi da shi

- Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yabi gwamnan jihar Edo

- Ya bukaci ragowar gwamnonin Najeriya da suyi koyi da shi

- Obsanjo ya bayyana haka ne yayin da ya ziyarci gwamnan a gidan gwamnatin jihar

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi ruwan kalaman yabo a kan gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, kamar yadda kamfanin dillancin labarai (NAN) ya rawaito.

Obasanjo ya bayyana cewar matukar Najeriya za ta cigaba to sai ragowar gwamnonin kasar nan sunyi koyi da gwamna Obaseki.

Obasanjo da gwamna Obaseki
Obasanjo ya yabi wani gwamna, ya bukaci ragowar gwamnoni su yi koyi da shi

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a jiya, yayin da shi da matar sa, Bola Obasanjo, suka ziyarci gwamna Obaseki a gidan gwamnatin jihar Edo.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Kaduna za ta kashe N337.19m domin horar da malaman makarantu

"Da ace kashi hamsin (50%) na gwamnonin Najeriya zasu zama masu kwazo kamar ka (Obaseki), da Najeriya ta samu cigaba cikin kankanin lokaci," inji Obasanjo.

Obasanjo ya ce rahotannin da yake karantawa a kan kokarin gwamnan sun gamsar da shi cewar gwamnan mai kishin jama'a ne.

Da yake bayyana dalilin zuwansa jihar, Obasanjo, ya ce ya ziyarci jihar domin gaisuwa da surukansa tare da yi wa gwamnan murnar shigowar sabuwar shekara.

Obasanjo ya bukaci gwamna Obaseki da ya cigaba da aiyukan alheri kamar yadda yake yi a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng