Kananan makamai na kara hura wutar rikicin manoma da makiyaya – in ji Dambazau
- Gwamnatin Najeriya ta nemi a kawo karshen yaduwar kananan makamai a yankin kasashen Afrika ta yamma
- Ministan harkokin cikin gida ya ce zaman lafiya a kasashen ECOWAS ba zai samu ba muddin aka zura ido kananan makamai na ci gaba da yawo
- Ministan ya bayyana cewa rikicin makiyaya da manoma ba a Najeriya kadai ake fama da ita ba
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta nemi hadin-kan kungiyar ECOWAS wajen kawo karshen yaduwar kananan makamai da ke barazanar ga zaman lafiya a yankunan kasashen Afrika ta yamma, da kuma Afirka baki daya.
Ministan harkokin cikin gidan Najeriya, Abdurrahman Bello Dambazau, Abdurrahman Bello Dambazau, a lokacin da ya kai ziyara hedikwatar kungiyar da ke birnin Abuja, ya bayyana cewa akwai tabbacin cewar yaduwar kananan makamai a kasashen yammacin Afrika na cikin abubuwan da ke kara hura wutar rikicin makiyaya da manoma a Najeriya.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari , ministan ya lura cewa tabbatar da zaman lafiya a yankin kasashen Afrika ta yamma ba zai samu ba muddin aka zura ido kananan makamai na ci gaba da yawo tsakanin kasashen.
Dambazau ya ci gaba da cewa rashin bin doka a iyakokin kasashen shi ma ya taka rawa wajen haifar da munanan rikicin makiyaya da manoma da ake samu a kasashen na ECOWAS.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Gambia, Adama Barrow
A nasa bangare, Alhaji lawali shuaibu,kwamishinan da ke kula da harkan kasuwanci da yawo cikin walwala na ECOWAS, ya bayyana cewa shaka babu sun gamsu da hujojjin Najeriya kuma nan gaba kadan za su shirya taro da zai mayar da hankali kan wadanan matsaloli domin duba matakan da ya kamata a dauka.
Rikicin makiyaya da manoma da ke sanadin rayuka da dama da kuma dukiyoyi masu yawa ba a Najeriya kadai ake fama da ita ba, hadda sauran kasashen kungiyar ECOWAS da kuma Afirka baki daya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng