Yan bindiga sun kai hari Taraba, sun kashe wani basarake

Yan bindiga sun kai hari Taraba, sun kashe wani basarake

- An rahoto cewa wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun kashe wani basarake a garin Karmen dake karamar hukumar Ibi na jihar Taraba

- Shugaban karamar hukumar Ibi mai rikon kwarya Bala Bako ya tabbatar da harin da kuma kisa

- Bako ya ce yan bindigan sun billo a yankin ne lokacin da suke shirin gudanar da wani ganawar tsaro

Wasu yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba sun kai hari ga al’umman Karmen karamar hukumar Ibi dake jihar Taraba da yammacin ranar Litinin, 15 ga watan Janairu inda suka kashe basaraken.

Shugaban karamar hukumar Ibi, Bala Bako, ya tabbatar da harin da kuma kisa a hirar wayar talho a Jalingo.

Bako ya bayyana ma manema labaranmu cewa yan bindigan sun auka garin ne yayinda mutanen garin ke shirin halartar wani taro akan harkar tsaro.

Yan bindiga sun kai hari Taraba, sun kashe wani basarake
Yan bindiga sun kai hari Taraba, sun kashe wani basarake

“Muna fuskantar wassu kalubale a fannin tsaro a Ibi kuma muna ta kokari don tabbatar da cewa kabilu a yankin sun karbi juna sun kuma zauna da junansu lafiya.

“Basaraken Ibi har ila yau ya kafa kwamiti wanda tattaunawa akan neman mafita ga kalubale a harkar tsaro, a halin taron ne yan bindiga suka kawo hari inda suka kashe basaraken."

KU KARANTA KUMA: Kwamishinan Ganduje ya amsa tambayoyi a hannun yan sanda kan wani bidiyo da ya saki game da Kwankwaso

Ya ce “Yayinda suka taru suna jiranmu don tattaunawa kan tsaro ne yan bindigan suka bayyana sannan suka soma harbe-harbe. Yan bindigan sun kashe basaraken ne a lokacin harin da sanduna."

Shugaban yankin wanda yace ya tura jami’an tsaro don dauke gawar yace, an kama wani da ake zargin da masaniya kan kisan sannan ana gudanar da bincike kan harin.

Yayinda yake magana kan kisan mutane takwas a kauyukan Gishiri da Dooshima da kuma daya a kauyen Danwaza a makon da ya gabata, Bako ya ce yan bindigan ne suka kai hari makwabtarta jihar Benue a yankunan Logo da Guma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel