Ba wanda zai shiga rigar Buhari a zaben 2019 - Sakon PDP zuwa ga gwamnonin APC

Ba wanda zai shiga rigar Buhari a zaben 2019 - Sakon PDP zuwa ga gwamnonin APC

Babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya watau PDP ta bayyana cewa shugaba Buhari ba zai iya tabukawa kowa komai ba a zaben shekara mai zuwa na 2019 kamar yadda yayi a zaben 2015.

Jam'iyyar ta bayyana haka ne a matsayin wani sako zuwa ga wasu gwamnonin jam'iyyar ta APC da aka ruwaito sunje sun gana da Buhari inda kuma suka roke shi da ya taimaka ya goya masu baya a zabe mai zuwa.

Ba wanda zai shiga rigar Buhari a zaben 2019 - Sakon PDP zuwa ga gwamnonin APC

Ba wanda zai shiga rigar Buhari a zaben 2019 - Sakon PDP zuwa ga gwamnonin APC

KU KARANTA: Rashin tsaro: Wani malami ya fadawa Buhari gaskiya

Legit.ng dai ta samu cewa mai magana da yawun jam'iyyar ta PDP ne dai mai suna Kola Ologbondiya shine ya bayyana hakan inda kuma ya kalubalanci jam'iyyar da ta gudanar da sahihin zabe a zaben mai zuwa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa gwamnoni bakwai daga jam'iyyar ta APC da suka hada da na Bauchi, Neja, Kaduna, Kogi da dai sauransu sun ziyarci Buhari inda suka jaddada goyon bayan su ga shugaban a zabe mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel