Har yanzu bamu samu wani ingantaccen shugabanci a Najeriya ba – Fafesa Ango Abdullahi

Har yanzu bamu samu wani ingantaccen shugabanci a Najeriya ba – Fafesa Ango Abdullahi

Tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello, kuma tsohon ministan noma, kuma shugaban kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullah ya koka kan tsarin shugaban kasa bai dace da Najeriya ba.

Daily Trust ta ruwaito Dattijon ya bayyana haka ne yayin wani taron gabatar da kasida don tunawa da mazan jiya, Ahmadu Sardauna da Tafawa Balewa, Inda yake fadin har yanzu ba’a samu ingantaccen shugabanci a Najeriya ba, kuma tsarin shugaban kasa bai tsinana ma Najeriya komai ba.

KU KARANTA: Yadda aka gudanar da bikin tunawa da ýan mazan jiya a jihar Kaduna

Har yanzu bamu samu wani ingantaccen shugabanci a Najeriya ba – Fafesa Ango Abdullahi
Fafesa Ango Abdullahi

Ango ya koka kan yadda Najeriya tayi watsi da shugabanci irin na ‘Firaiminista’, kamar wanda Tafawa Balewa yayi a zamaninsa, daga 1960-1966, muka rungumi tsarin shugaban kasa, yace haka bai dace ba, inji shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban taron, Alhaji Ibrahim Coomassie ya danganta matsalar Najeriya ga shugabanci, inda yace muddin aka cigaba a haka, toh lallai wata rana kasar zata watse.

Daga cikin manyan baki da suka halarci zaman akwai tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da kuma tsohon Alkalin Alkalai, Mai shari’a Mamman Nasir.Ku biyo mu a

https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng