Siyasa: Secondus ya gargadi gwamnatin APC a kan maganganun ƙiyayya

Siyasa: Secondus ya gargadi gwamnatin APC a kan maganganun ƙiyayya

- Shugaban jam’iyyar PDP ya gargadi gwamnatin APC a kan maganganun ƙiyayya

- Shugaban ya yabawa rundunar sojojin kasar wajen murkushe ‘yan kungiyar Boko Haram

- Secondo ya ce Najeriya ta kasance kasa daya ne a yau saboda gudunmawar rundunar sojojin kasar

Shugaban jam'iyyar PDP, Prince Uche Secondus, ya gargadi ‘ya’yan jam’iyya mai mulki ta APC, game da maganganun ƙiyayya da ke kawo rashin zaman lafiya a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da aka bayar a ranar Lahadi, 14 ga watan Janairu na sakon ranar tunawa da rundunar sojoji na wannan shekara, Secondus ya yaba wa rundunar sojojin kasar wajen murkushe ‘yan kungiyar Boko Haram, yayin da ya kuma cajirce su da su mayar da hankali a kan yadda za’a samu hadin kai tsakanin al’ummar Najeriya.

Shugaban ya bukaci 'yan Najeriya su nuna godiya da goyon baya ga mazan jiya wadanda suka sadaukar da kansu don tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Siyasa: Secondus ya gargadi gwamnatin APC a kan maganganun ƙiyayya

Shugaban jam'iyyar PDP, Prince Uche Secondus

Ya ce "Najeriya ta kasance kasa daya ne a yau saboda gudunmawar rundunar sojoji don ta ci gaba da kasancewa kasa daya”.

KU KARANTA: Yadda aka gudanar da bikin tunawa da ýan mazan jiya a jihar Kaduna (Hotuna)

"Ya kamata 'yan Najeriya musamman ‘yan siyasa su yaba da babbar gudummawar sojojinmu musamman wadanda suka sadaukar da ransu don kishin kasar”.

"Ya kamata gwamnatin tarayya a karkashin jam’iyyar APC su kauce wa ƙiyayya da girman kai a cikin maganganunsu”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel