Sifeto janar ya ziyarci garin Tunga bayan gwamna Ortom ya yi zargin an rabawa matasan garin bindigu

Sifeto janar ya ziyarci garin Tunga bayan gwamna Ortom ya yi zargin an rabawa matasan garin bindigu

- Gwamna Ortom ya yi zargin an rabawa wasu matasa a garin Tunga bindigu

- Babban Sifeton hukumar 'yan sanda ya isa garin domi tabbatar da zargin

- Dattijan garin sun karyata zargin gwamnan

A kokarinsa na tabbatar da zargin da gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya yi, na cewar an rabawa wasu matasa a garin Tunga bindigu domin su kara tayar da hankula a jihar, babban Sifeton 'yan sanda, Ibrahim Idris, ya isa garin da kansa domin tabbatar da gaskiyar zargin.

Sifeto janar na 'yan sanda ya ziyarci garin Tunga bayan gwamna Ortom ya yi zargin an rabawa matasan garin bindigu

Sifeto janar na 'yan sanda yayin ziyarar garin Tunga

Idris ya isa garin Tunga a ranar Asabar inda ya samu ganawa da Sarkin garin Tunga, Alhaji Muhammad Ibrahim Shuaibu, da kuma shugaban kabilar Tiv dake garin, Abraham K. Vighe; wanda dan uwa ne ga kwamishinan noman jihar, James Abwe, kazalika, shugaban kungiyar kabilar Fulbe a jihar Benuwe, Ardo Laminu ya halarci taron.

Sifeto janar na 'yan sanda ya ziyarci garin Tunga bayan gwamna Ortom ya yi zargin an rabawa matasan garin bindigu

Sifeto janar na 'yan sanda a garin Tunga

Bakin dukkanin shugabannin ya zo daya wajen tabbatarwa da Idris cewar zargin gwamnan ba gaskiya ba ne, tare da bayyana masa cewar dokar gwamnan ta hana kiwon dabbobi ta jawo rikicin da jihar ke fama da shi.

DUBA WANNAN: Idan sulhu bai yi aiki ba, zamu dau tsattsaurin mataki - Gwamna Akeredolu

Tun cikin da ya wuce ne shugaba Buhari ya umarci Sifeto janar na 'yan sanda da ya tattara kayansa ya koma jihar Benuwe har sai zaman lafiya ya dawo, umarnin da Sifeton ya amsa ba tare da wani bata lokaci ba.

Sifeto janar na 'yan sanda ya ziyarci garin Tunga bayan gwamna Ortom ya yi zargin an rabawa matasan garin bindigu

Sifeto janar na yayin da ya ziyarci garin Tunga

Ya zuwa yanzu al'amura sun fara lafawa a jihar Benuwe, zaman lafiya ya fara yankunan da haren-haren makiyaya ya shafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel