Miji ya kunna wutar rikici tsakanin matarsa da wata, wutar ta hallaka ɗan ba ruwana

Miji ya kunna wutar rikici tsakanin matarsa da wata, wutar ta hallaka ɗan ba ruwana

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya dake babban birnin tarayya Abuja sun cika hannu da wata mata, wanda ta kasha dan bazawarar mijinta da wuka a garin Kubwa, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito matar mai suna Rakiat Abdulkarim ta fita gidanta dake garin Gauraka da misalin karfe 10 na daren Alhamis 11 ga watan Janairu, inda ta nufi garin Kubwa don gane ma idonta wainar da mijinta ke toyawa a gida bazawararsa.

KU KARANTA: Sai na mulki Najeriya ko ta wani hali – Inji wani babban Fasto

Ai kuwa da isarta gidan, sai ta tarar da motar mijinta a kofar gidan bazawarar tasa, nan da nan ba tare da bata lokaci ba ta kunna kai cikin gidan, sai ko aka fara cacar baki tsakanin Rakiat da bazawarar, inda Rakiat ta huce a kan dan matar mai shekaru 17, ta hanyar caka masa wuka.

Uwar yaron ta yi Karin bayani kamar haka: “Ni ma’aikaciyar jinya ce, kuma ni ke duba iyalan wannan mutumi a duk lokacin da basu da lafiya, saboda sun taba zama makwabtanmu a baya kafin su tashi, a gaskiya na sha fada ma matar nan, in dai ta ga mijinta a nan, magani nake bashi. Don haka lokacin da ta zo ma baya nan.”

Matar ta cigaba da fadin a lokacin da Rakiat ta shigo tana ihu, yarona Auwal na barci, ihunta yasa shi farkawa, sai ya leko waje don jin me yake faruwa, fitarsa kenan ta sassare shi da wuka, daga nan muka garzaya da shi babban Asibitin Kubwa, inda ya cika da misalign karfe 12 na dare.

A nasa jawabin, DPO na Yansandan yankin, Ayobami Surajuddee ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace wasu matasan unguwar cikin fushi mutuwar yaron sun farfasa motar mutumin, sa’annan yace Yansanda sun kama Rakiat, kuma tuni aka binne mamacin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel