Tsananin soyayyar iyayen zamani ga 'ya'ya ne silar mace-macen aure - Hajiya Bilkisu Ahmed Funtuwa

Tsananin soyayyar iyayen zamani ga 'ya'ya ne silar mace-macen aure - Hajiya Bilkisu Ahmed Funtuwa

- Bincike ya nuna cewa mutuwar Aure ya zama ruwan dare a kasar Hausa

- Wasu iyaye mata kuma shahararrun marubutan litattafan Hausa sun ce tabarbarewar tarbiyya ce silar mace-macen aure a yankin Hausawa

Yawan mutuwar aure tsakanin al’ummar Hausawa ya zama tamkar ruwan dare a yanzu, wanda al’amarin ba haka yake ba a shekarun baya.

A wata tattauna da BBC Hausa ta yi da iyaye mata, kuma shahararrun marubutan litattafan Hausa a arewacin Najeriya wato, Hajiya Balaraba Ramat Yakubu da kuma Hajiya Bilkisu Ahmed Funtuwa sun bayyana asalin abubuwan dake janyo mace-macen aure kasar Hausawa.

'Tsananin soyayyar iyayen zamani ga 'ya'ya ne silar mace-macen aure'
'Tsananin soyayyar iyayen zamani ga 'ya'ya ne silar mace-macen aure'

Marubutan sun ce lalacewar tarbiyyar Hausawa ta samu asali ne daga irin soyayyayar da iyayen zamani suke nuna wa ‘ya’yan su ce babban abun dake janyo mace-macen aure.

KU KARANTA : 'Yan Najeriya guda 560 da suka dawo daga kasar Libya sun isa filin jirgin saman Fatakol

Sun kara da cewa, matsaloli kamar yawan amfani da kafofoin sada zumunta na zamani, yawan kallon fina-fina ketare, zurfafa soyayya don abun duniya, da shaye-shayen miyagun kwayoyi da matsananci kishi suna cikin abubuwan dake kashe aure a kasar Hausa.

Iyayen sun kuma ce matukar gwamnati ba ta sa hannu a cikin wannan lamarin ba, nan da shekaru kadan al'ummar arewacin Najeriya za ta samu kanta a halin da ya fi na yanzu muni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel