2019: Ba zan bi sahun Atiku ba, ina APC daram dam-dam – In ji Mama Taraba

2019: Ba zan bi sahun Atiku ba, ina APC daram dam-dam – In ji Mama Taraba

- Mama Taraba ta musanta zargin cewa tana shirin ficewa daga jam’iyyar APC

- Ministan ta yi alkawarin amincewa da shugaba kasa, Muhammadu Buhari

- Mama Taraba ta ce Atiku uban gidan ta ne tun kafin ta shiga siyasa kuma idan ya ce zai tsaya takara za ta goyi bayansa

Abokan hulɗa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kuma ministan harkokin mata, Aisha Alhassan, wanda aka fi sani da ‘Mama Taraba’ ta musanta zargin cewa tana shirin yin watsi da jam'iyya mai mulki ta APC.

Ministan ta kuma yi alkawarin amincewa da shugaba Muhammadu Buhari, tana mai cewa "Na kasance kuma zan ci gaba da zama a APC".

Idan dai baku manta ba Mista Abubakar ya koma jam'iyyar PDP a watan Disamban da ta gabata.

2019: Ba zan bi sahun Atiku ba, ina APC daram dam-dam – In ji Mama Taraba
Ministan harkokin mata, Aisha Alhassan, wanda aka fi sani da ‘Mama Taraba’
Asali: Facebook

An siffanta cewa, Misis Alhassan, tsohon dan majalisar dattawa, da sauran abokan hulɗa na tsohon mataimakin shugaban kasa zasu kasance tare da shi a PDP.

KU KARANTA: Fasto Tunde Bakare ya yi kakkausar suka a kan gwamnatin Buhari

Tun da farko a watan Satumbar da ta gabata, ta ce za ta goyi bayan Mista Abubakar a zaben shugaban kasa na shekarar 2019 koda kuwa shugaba Muhammadu Buhari ya yanke shawarar zai fito takara.

Ta ce, "Atiku uban gida na ne tun kafin in shiga siyasa", ta fada hakan a harshen Hausa. "Bugu da ƙari, Baba Buhari bai gaya mana cewa zai zarce a shekarar 2019 ba".

"Bari in gaya maka a yau cewa idan Baba ya ce zai tsaya takara a shekara ta 2019, na rantse da Allah, zan je gabansa na durƙusa a gabansa kuma in gaya masa cewa 'Baba na gode wa damar da ka ba ni a gwamnatinka a matsayin minista, amma Baba kamar yadda ka sani Atiku ne kawai zan marawa baya domin shi ne uban gida na. Idan Atiku ya ce zai tsaya takara".

A cikin hira a wayar tarho da majiyar Legit.ng, ministan wanda aka fi sani da Mama Taraba ta ce babu wanda ya tilasta barin PDP, a karkashin jam’iyyar da ta zama sanata, cewa tana nan daram a APC.

"Zan ci gaba da yi wa jam’iyyarta aiki, saboda haka yasa na tafi Taraba don neman nasarar dan takarar jam'iyyar mu Sanusi Jambawaile”.

"Na san mutane da yawa suna so su ga na bar APC, amma bari in tabbatar da cewa ina nan daram dam-dam a APC”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel