Na sayi bindiga daga hannun abokina N9,000 – Mai bada hayan bindiga ga barayin babur
- An damke barayin babur 3 a jihar Legas
- Sun bayyana wanda ke basu hayan bindigogi domin fashi
Hukumar yan sandan Rapid Response Squad na jihar Legas ta damke matasa masu kwace babur a hannanun yan achaba 3 a kwaryan jihar.
Matasan masu suna, Taiwo Lawal (mai shekara 23), Kabiru Ajiboye (mai shakaru 24) and Seyi Ayetoba (mai shakaru 27) sun shiga hannu ne a daren Alhamis a unguwar Somolu yayinda suke kokarin kwacewa wani babur.
Dan achaba da fasinja da akayiwa kwace sun daga murya wanda ya jawo hankalin jami’an yan sanda inda aka kure musu gudu tare da gudunmuwar mutanen unguwa.
Bayan an damke su, sun bayyana cewa wani Ridwan Omole ne ke basu hayan bindiga. Ba tare da bata lokaci ba, hukumar ta far masa a gidan iyayensa inda suka damke shi.
DUBA WANNAN: Sabon rikici tsakanin Hausawa da wasu matasa ya kara barkewa a jihar Benuwe
Matasan sunce sukan kwace babur ne a unguwan Ajah, Costain, Onipanu, Yaba da National Stadium kuma sukan sayar da babur din tsakanin N60,000 da N30,000
Makaman da aka samu a hannunsu ya kunshi karamar bindiga, 9mm A - K47 da wuka.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng