'Yan Najeriya guda 560 da suka dawo daga kasar Libya sun isa filin jirgin saman Fatakol

'Yan Najeriya guda 560 da suka dawo daga kasar Libya sun isa filin jirgin saman Fatakol

- 'Yan gudun hijira da suka dawo daga kasar Libya sun isa birnin Fatakol

- Shugaban hukumar NEMA na yankin kudu maso kudu ya bayyana takaicin sa akan irin mumunar tarbar da wasu jihohi suke yiwa mutanen su da suka dawo daga kasar Libya

Kashi na uku daga cikin 'yan gudun hijiran Najeriya guda 560 da suka dawo daga kasar Libya sun isa filin jirgin saman Fatakol.

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa NEMA reshen yankin kudu maso kudu, Martins Ejike, ya sanar da yan jarida haka a ranar Asabar a Fatakol.

'Yan Najeriya guda 560 da suka dawo daga kasar Libya sun isa filin jirgin saman Fatakol
'Yan Najeriya guda 560 da suka dawo daga kasar Libya sun isa filin jirgin saman Fatakol

Ejike ya ce, daga cikin mutanen da suka iso filin jirgin saman birnin Fatakol, akwai kananan yara 20 da manya 540 da jirgin saman Max Air mai lamba 5N-HMM ya kawo su da misalin karfe 11:52 na yamma.

KU KARANTA : Kira ga Kristocin Najeriya : Kowa ya shiga siyasa gadan-gadan - Kungiyar CAN

Ya bayyana takaicin sa akan irin mumunar tarbar da wasu jihohi suka yiwa yan gudun hijira da suka dawo daga kasar Libya.

Ejike yace gwamnatin tarayya ta ba jihohi wa'adin sa’o’i 48 su kwashe duka yan gudun hijira jihohin su da suka dawo daga kasar Libya a sansanin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng