Mazauna Jalingo sun shiga tashin hankali kan barazanar makiyaya na kai hari garin
- Mazauna Jolly Nyame dake Jalingo, jihar Taraba sun gudu daga gidajensu
- Sun tsere ne bayan labarin da suka ji cewan makiyaya suna shirin kawo hari akan al’umman
Al’umman Jolly Nyame a garin Jalingo, jihar Taraba sun fada cikin rudani sannan kuma yawancin mazauna garin a halin yanzu sunyi gudun hijira daga gidajensu a ranar Lahadi, 15 ga watan Janairu bayan labarin da ya kai garesu cewan makiyaya suna shirin kaiwa al’umman garin hari.
Al’umman sun bar gidajensu bayan wani jami’in tsaro ya shawarcesu da su gudu su nemi kariya saboda shiri da makiyaya ke yi na kawo hari ga al’umma cikin dare.
Wani mazaunin garin yayi magana da manema labarai kamar haka: “Ina a gida ina kallon wasan kwallon kafar Liverpool da Manchester a lokacin da matana ta shigo ta fada mun ana shirin kawo hare-hare. A halin yanzu da nake muku magana, sai da muka gudu tare da yaranmu don kariya.
“Wani jami’in tsaro ya shawarcemu da mu bar yankin, a halin yanzu muna gudun hijira amman zamu tabbatar da al’amarin abubuwa da safe.”
Jaridar Premium Times, duk da haka ta rahoto cewa rundunan yan sanda a jihar sun karyata duk wani shirin hari na makiyaya.
Mai magana da yawun yan sanda, David Misal, ya ce: "Babu tashin hankali a Jalingo. Ayyuka suna tafiya kamar yanda aka saba.”
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng