Dandalin Kannywood: Buruka na sun cika, saura aure kawai yanzu - Aisha Tsamiya

Dandalin Kannywood: Buruka na sun cika, saura aure kawai yanzu - Aisha Tsamiya

Fitacciyar jarumar wasan Hausa ta fina-finan Kannywood watau Aisha Aliyu da aka fi sani da Aisha Tsamiya ta bayyana cewa yanzu kam burikan ta a rayuwa duka sun cika saura aure kawai.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da ta yi da majiyar mu a karshen mako inda ta bayyana cewa dama can burin da take da shi shine karatu wanda kuma tuni tayi nisa a cikin sa.

Dandalin Kannywood: Buruka na sun cika, saura aure kawai yanzu - Aisha Tsamiya
Dandalin Kannywood: Buruka na sun cika, saura aure kawai yanzu - Aisha Tsamiya

Legit.ng ta kuma samu daga jarumar bugu da kari cewar ta bayyana rade-raden da ake yi na cewa 'yan fim basa son aure a matsayin labarin kanzon kurege da tace bai da tushe balle makama.

Jamrumar ta bayyana cewa silar aure ne ya sa suka zo duniya don haka kuwa ba yadda za'ayi ta guji aure sannan kuma daman cikar darajar mace yanzu a duniya shine a dakin mijin ta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng