Rundunar sojin Najeriya ta siya motocin yaki daga kamfanin Innoson na Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta siya motocin yaki daga kamfanin Innoson na Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta fara daukar motocin yakin da ta siya daga kamfanin kera motocin nan na dan Najeriya mai suna Innoson domin cigaba da fatattakar 'yan ta'adda a duk inda suke.

Mun samu wannan labarin ne dai daga shafin dandalin sada zumunta na Facebook mallakin jami'in hulda da jama'a na rundunar Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka wanda ya watsa hotunan motocin yakin.

Rundunar sojin Najeriya ta siya motocin yaki daga kamfanin Innoson na Najeriya
Rundunar sojin Najeriya ta siya motocin yaki daga kamfanin Innoson na Najeriya

Rahotannin da ke zuwa mana na nuni ne da cewa jami'an sojin saman Najeriya sun sanar da kammala siyo manyan jiragen yakin idasa fatattakar 'yan kungiyar Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriya ta siya motocin yaki daga kamfanin Innoson na Najeriya
Rundunar sojin Najeriya ta siya motocin yaki daga kamfanin Innoson na Najeriya

Rundunar dai ta bayyana cewa ta siyo jiragen yakin ne daga kasar Pakistan dake a yankin gabashin duniya bayan lokaci mai tsawo da ta dauka tana cinikin su.

Legit.ng dai ta samu cewa kasar Najeriya ta karkata akalar cinikin makaman yaki da jirage ne daga kasar Amurka biwo bayan wani rashin jituwa da ta samu da gwamnatin inda kuma ta ayyana kin amincewa da sayar mata din.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng