Ke Duniya: Karanta ta’asan da gungun yan fashi da makami suka tafka ma wata Tsohuwa

Ke Duniya: Karanta ta’asan da gungun yan fashi da makami suka tafka ma wata Tsohuwa

Runfunar Yansandan jihar Edo sun cika hannu da wani matashi mai shekaru 23, mai sana’ar fashi da makami biyo bayan samun rahoton ya hada kai da wan mutumi sun yi ma wata tsohuwa fashi.

Wannan dan fashi mai suna Kngsley Orion ya fada gidan wannan tsohuwa mai shekaru 89 ne a ranar 17 ga watan Nuwamba tare da abokinsa Ehiati Osaretin, inda suka yi ma tsohuwa Imasogbonre Enahoro da yarta Maroline Ajibola, karkaf.

KU KARANTA: Labari da Duminsa: Anyi jina-jina a sabon rikici tsakanin 'yan Gandujiyya da 'yan Kwankwasiyya a jihar Kano

Daily Trust ta ruwaito, tsabar rashin Imani, barayin sai suka shigar da tsohuwa tare da yarta cikin bayi, inda suka daure su, sa’annan suka manne musu baki da sinadarin ‘Super Glue’ wai don kada su yi ihun neman ceto.

Uwargida Enahoro fadi cewa “Kalli wannan yaron daya manne min baki da gam, sa’annan ya daure ni kamar wata zamo, ya dinga mari na tare da jefa ni cikin bayi.” Kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito ta. Sai dai tsohuwa Enahoro ta farfado bayan kwashe sati biyu tana jinya a Asibiti.

Da take mayar da jawabi, diyar wannan tsohuwa, Ajibola ta ce: “Shigowa na kenan cikin gida sai na tarar da barayin sun tsare mahaifiyata, sai nima suka kama ni, suka daure mu gaba daya, sa’annan suka arce da mota ta kirar Camry, har sai da mijina ya zo ya cece mu.”

Matashin dan fashin ya tabbatar da amsa laifin sa, inda yace yayi hakan ne da niyyar sama ma kansa kudin makaranta, amma da suka je gidan, sai basu samu kudi ba, wannan ne ya sa suka saci motar matar.

Daga karshe Kwamishinan Yansandan jiha ya bayyana cewa zasu gurfanar da wadanda ake zargi gaban Kotu da zarar sun kamala gudanar da bincike a kan su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel