Tsuguni bata kare ba: Wani sabon rikici tsakanin Hausawa da wasu matasa ya kara barkewa a jihar Benuwe
- Rikici ya barke tsakanin wasu matasa da Hausawa a Makurdi
- Hatsarin mota ne sababin barkewar rikicin
- Harkokin kasuwanci sun tsaya cik a yankin da abin ya shafa
Wani sabon rikici mai nasaba da kabilanci ya kara barkewa a jihar Benuwe tsakanin wasu matasa da Hausawa a yankin Wadata dake garin Makurdi, babban birnin jihar Benuwe.
Wani ganau ya shaidawa jaridar TheCable cewar rikicin ya samo asali ne bayan wata mota ta kade wani bafulatani kuma ya mutu nan take a titin bakin kasuwar Wadata.
Matasa da yawa sun samu raunuka sakamakon rikicin. Kazalika an kwankwatse motaci da dama.
Jami'an 'yan sanda sun yi dirar mikiya a wurin da rikicin ya barke, kuma sunyi ruwan barkonon tsohuwa.
DUBA WANNAN: Abinda na fadawa gwamnan jihar Benuwe a kan hare-haren makiyaya yayin ganawar mu - Buhari
Akwai Hausawa da Fulbe masu yawa a yankin na Wadata dake Makurdi, inda kwatar garin take.
Barkewar rikicin ta jawo tsayawar harkokin kasuwanci a wurin.
Babu wani rahoto daga hukumar 'yan sanda dangane da barkewar rikicin.
Jihar Benuwe na fama da rigingimu tsakanin makiyaya da manoma, dalilin da ya saka shugaba Buhari umartar babban Sifeton 'yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, komawa jihar har sai an shawo kan matsalar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng