'Yan Najeriya 14 da aka yankewa hukuncin kisa a Madinah sun aiko wa da Buhari sako
- An garkame wasu 'yan Najeriya su 14 a kurkukun Madinah
- Ana zarginsu da tu'ammali da miyagun kwayoyi a kasar Saudiyya
- Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da shiga cikin maganar
Wasu 'yan Najeriya su 14 da aka tura kurkuku a Madinah ta kasar Saudiyya sun aiko wa shugaba Buhari sakon neman taimako domin ya kubutar da su daga wukar hauni.
Ana tuhumar 'yan Najeriyan ne da tu'ammali da miyagun kwayoyi a kasar Saudiyya, kuma kasar tana zartar da hukuncin kisa ne ga duk wadanda suka aikata irin wannan laifi. Saidai 'yan Najeriya sun tsorata bayan an tura su gidan yari, suna masu cewar basu aikata laifin ba kuma kasar ba zata yi masu adalci ba.
"Mun san kashe mu zasu yi, muna rokon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo mana agaji, a duba tuhumar da suke yi mana domin ba zasu bama damar kare kan mu ba."
Daga cikin 'yan Najeriya dake kurkukun akwai: Lolo Babatunde, Biola Lawal, Hafis Amosu, Jimoh Ishola, Tunde Ibrahim, Abdurimi Aweda, Adam Abubakar, Amode Tunde, Adewumi Adepoju, Saka Riyau, Aliu Muhammed, Abdul Raman, Yekini Yahaya da kuma wasu mata guda biyu. Akwai karin wasu 'yan Najeriya dake gidajen yari a Riyadh da Makkah a kasar Saudiyya.
DUBA WANNAN: 'Yan ci-rani 200 daga Najeriya da wasu kasashen Afrika sun dulmiye a teku
Wadanda ake tuhumar sun tuntubi ofishin jakadancin Najeriya dake Riyadh da kokon barar a taimake su kafin kasar ta Saudiyya ta zartar masu da hukuncin.
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewar tana da masaniyar daurin 'yan Najeriya a kurkuku a kasar Saudiyya bisa zarginsu da tu'ammali da miyagun kwayoyi. Minista harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, ya tabbatar da cewar gwamnatin Najeriya na daukan matakan da ya dace domin tattaunawa da hukumomin kasar Saudiyya a kan makomar 'yan Najeriyan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng