Kasashen Afrika da ake yaren Hausa

Kasashen Afrika da ake yaren Hausa

- Yaren Hausa na daga cikin manyan yarukan nahiyar Afrika

- Najeriya ce tafi yawan Hausawa a Duniya

- Akwai fiye da mutum miliyan 38 dake yaren Hausa a duniya

Yaren Hausa na daga cikin manyan yarukan nahiyar Afrika. Har yanzu ba'a samu takamaiman tarihin asalin yaren Hausa ba, masana da yawa sun yi kokari wajen kawo tarihin asalin yaren Hausa da Hausawa.

Wani bincike ya nuna cewar akwai kimanin mutum miliyan 38 dake yaren Hausa a fadin duniya. Akwai Hausawa a kasashen duniya da dama, kuma bincike ya nuna sunyi hijira ne daga kasashen Afrika ya zuwa sauran kasashen nahiyoyin duniya.

Kasashen Afrika da ake yaren Hausa

Hausawa

Kasancewar yaren Hausa yare ne dake da tushe a nahiyar Afrika, hakan ne ya saka muka kawo maku jerin wasu kasashen Afrika da yaren na Hausa ya ratsa da kuma adadin Hausawa dake kasashen.

1. Najeriya - 24,448,000

2. Nijar - 9,834,000

3. Benin - 1,058,000

4. Kwadebuwa - 385,000

5. Kamaru - 357,000

DUBA WANNAN: Hukumar tantance fina-finan Hausa ta janye dakatarwar da ta yiwa Rahama Sadau

6. Chadi - 274,000

7. Ghana - 269,000

8. Sudan - 110,000

9. Togo - 20,000

10. Gabon - 12,000

11. Aljeriya - 11,000

12. Kongo - 9,400

13. Burkina Faso - 2,700

Wadannan kasashe ba iyakacin kasashen duniya kenan da yaren Hausa keda yawan jama'a ba, saidai tunda yaren na Afrika ne kuma ragowar Hausawa dake kasashen da ba na Afrika ba zuwa suka yi, shi yasa bamu saka su cikin wannan lissafi ba.

Muna saka ran wani lokacin zamu kawo maku jerin kasashen duniya da Hausawa da yaren Hausa keda tasiri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel