To fa: Gardama ta kaure a kan wata ‘yar Musulma da ta yi rida a Jos

To fa: Gardama ta kaure a kan wata ‘yar Musulma da ta yi rida a Jos

- Ana cece-kuce a kan wata ‘yar Musulma da ta yi rida a garin Jos

- Yarinyar, 'yar wani basarake ne a garin Biu da ke jihar Borno

- Mahaifin wannan yarinyar ya ce sam bai yarda da hakan ba

Ana kai ruwa rana a kan wata ‘yar Musulma da ta yi rida zuwa addinin Kirista kamar yadda mahaifin yarinyar ya shaida cewa ya bukaci hukumar jami’an ‘yan sandan farin kaya (SSS) shiga tsakani , wanda aka yi zargin cewa sun kama saurayi ita yarinyar, Injiniya Simput Eagles Dafup a jihar Filato.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari Nabila Umar Sanda, mai shekaru 18 da haihuwa, kuma 'yar wani basarake a garin Biu, jihar Borno, wanda aka yi zargin cewa sace a birnin Abuja ranar 1 ga watan Disamba, 2017.

Yayin da mahaifin Nabila bai ji duriyar ta ba, wanda aka ce ta gama karatu a Kwalejin sojojin sama wato ‘Air Force Comprehensive College’, Jos kuma daliba a jami'ar Bingham a jihar Nasarawa.

To fa: Gardama ta kaure a kan wata ‘yar Musulma da ta yi rida a Jos
Fasto Jerry Datim, yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai

Rahotanni sun bayyana cewa mahaifinta ya sanar da jami’an SSS cewa 'yarsa ta bace, bayan wannan lokacin aka gano ta a wani gidan fasto Jerry Datim a Jos.

KU KARANTA: An gudanar sa Sallar jana'izar jarumin soja, Manjo MM Hassan

Duk da haka, Datim ya shaida wa majiyar Legit.ng a kan waya cewa Nabila ta karbi addinin Kirista a lokacin da ta ke jami'ar Bingham kuma ta sadu da Dafup, wani malami a Ghana shekaru hudu da suka wuce a cikin jirgin sama zuwa Dubai.

Fasto ya ce Nabila a kwanan nan tare da Dafup sun sake haduwa a lokacin da ya ziyarci Jos don bikin Kirsimeti kuma ta bayyana manufarta.

Fasto Jerry ya kara bayyana cewa ko da yake mahaifin Nabila ya san da batun, amma ya ce bai yarda da hakan ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel