Kashe-Kashe: Kwamitin majalisar dattawa ya dirfafa a jihar Benue
A halin yanzu, kwamitin majalisar dattawa akan harkokin tsaro ya dirfafa a jihar Benuwe domin gudanar da binciken diddigi akan salwantar rayuka da asarar dukiya da makiyaya ke gadarwa a jihar.
Daya daga cikin mambobin kwamitin, Sanata Biodun Olujimi mai wakiltar Kudancin jihar Ekiti, ta shaidawa manema labarai a ranar Juma'ar da ta gabata cewa, tuni ta dirra a jihar da sauran mambobin kwamitin.
'Yar majalisar ta bayyana cewa, kwamitin zai gana a ranar asabar ta yau da gwamnan jihar Samuel Ortom, shugaban kabilar Tibi, hukumomin tsaro, shugabannin al'ummomi da kuma masu ruwa da tsaki akan al'amuran.
Olujimi ta bayyanawa 'yan jaridar cewa, tawagar tasu ta kutsa cikin jihar ne domin samun cikakken bayanai dangane da hare-haren makiyaya da suka salwantar da rayuka 73 a jihar.
Legit.ng ta fahimci cewa, majalisar dattawa tana ci gaba da hutun kirsmeti da na sabuwar shekara, inda zata dawo bakin aiki a ranar talatar mako mai gabatowa.
KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun tarwatsa kan wani mutum a birnin Ibadan
A yayin haka ne shugaban majalisar, Dakta Bukola Saraki, ya umarci kwamitin akan katse musu hutu tun a ranar larabar da ta gabata, domin gudanar da bincike dangane da hare-haren jihar Benuwe da Ribas, inda majalisar zata fara bi ta kai a yayin dawowarta a mako mai gabatowa.
Wannan umarni yazo ne a wata sanawar daren ranar larabar da ta gabata da sanadin mai magana da yawun shugaban majalisar, Mista Yusuph Olaniyonu.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng