Baba Ahmed: Dan kasar Mauritaniya wanda ya kafa daula a Najeriya

Baba Ahmed: Dan kasar Mauritaniya wanda ya kafa daula a Najeriya

Dangin Baba Ahmed sun shahara a Arewacin najeriya da kuma kasa ga baki daya. Kwarewa da kokari da jajircewa da yan gidan keyi ya daga sunan dangin a Najeriya.

A matsayinsa na dan kasuwan dabbobi daga kasar Mauritaniya, Baba Ahmed ya gina babban dangi a Arewacin Najeriya.

Yaran Baba Ahmed dake raye yanzu 22 ne. Danhin ta rasa mahaifin da yara 11 a shekarun baya. Mambobin dangin sun yi suna a bangarori daban-daban na rayuwa musamman a Arewacin Najeriya.

Duk da ilimi addinin marigayi Baba Ahmed, bai haramtawa yayansa karatun Boko ba, bal ya taimaka musu iya matuka wajen tabbatar da cewa sun samu isasshen ilimi.

Baba Ahmed: Dan kasar Mauritaniya wanda ya kafa daula a Najeriya
Baba Ahmed: Dan kasar Mauritaniya wanda ya kafa daula a Najeriya

Sabanin Dakta Mahmoon Baba Ahmed, Mahadiyya Baba Ahmed ce babbar gidan kuma ta bayyanawa jaridar Daily Trust cewa mahaifinsu ya haifi dukkan yaransa 33 ne a gidansu da ke No. 17 Baba-Ahmed Road, Tudun Wada, Zaria ko masaukin ma'aikata da ke kwalejin Barewa.

Daga cikin yaransa da suka shahara sune Abdulmalin Baba Ahmed, wanda shine diraktan gidan talabijin DITV/Alheri Rediyo a jihar Kaduna, Datti Baba Ahmed wanda tsohon sanata ne kuma mai jami'ar Baze da ke Abuja.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun yi ram da matsafa 'yan yankan kai a Osun

Sauran sune Abdus-salam wanda tsohon shugaban karamar hukumar Zaria kuma kwamishana a jihar Kaduna, Abdulrashid Baba Ahmed wanda drikata ne a ma'aikatar shari'a, Mahmoon Baba Ahmed wanda babban dan jarida ne a FRCN, sai Dakta Hakim Baba Ahmed wanda yayi sakataren din-din-din a hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC kuma a yanzu babban ma'aikacin shugaban majalisar dattawa ne.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng