Akalla mutun daya ya mutu a wata rikici tsakanin Hausawa da Fulani a Sakkwato

Akalla mutun daya ya mutu a wata rikici tsakanin Hausawa da Fulani a Sakkwato

- Rikici tsakanin Hausawa da Fulani ta yi sanadiyar mutuwar wani dattijo a Sakkwato

- Wannan rikicin ta barke ne a lokacin da wani bafilatani ya soki mai sayar da rake a kan wani sabani tsakaninsu

- Wasu 'yan bindiga sun yi amfani da wannan damar inda suka fashe shaguna da dama kuma suka yi awon gaba da dukiyoyin jama’a

Rahotanna sun bayyana cewa wani dattijo ya rasa ransa yayin da wata rikici ta barke tsakanin Fulani da al’ummar Hausawa a Kasuwan Wawuri da ke yankin karamar hukumar Tangaza a jihar Sakkwato.

Majiya Legit.ng ta fahimci cewa rikicin ya fara ne kimanin karfe 1:30 na yamma a lokacin da wani bafilatani ya soki mai sayar da rake a kan rashin fahimta.

Kakakin hukumar 'yan sandan, ASP Ibrahim Abarass, wanda ya tabbatar da wannan lamarin ga majiyarmu, ya ce rikicin ya fara ne lokacin da mai sayar da rake ya tambayi bafilatanin kudinsa bayan ya dauki rake a matsayin zai saya.

Akalla mutun daya ya mutu a wata rikici tsakanin Hausawa da Fulani a Sakkwato
Rikici

Hukumar ta bayyana cewa bayan da ta kame mutumin da ake zargi da aikata laifin da kuma tsare shi, zai dangin wanda aka azabtar suka zo suka kwace shi sa’a nan aka masa duka. Sanadiyar wannan mataki ne ya sa fada ta barke a cikin kasuwa.

KU KARANTA: Rikicin Makiyaya: Lalong karya yake, na kalubalance shi a wayan tarho - Samuel Ortom

Majiyarmu ta tabbatar cewa a nan ne 'yan bindiga suka yi amfani da wannan damar inda suka fashe shaguna da dama kuma suka yi awon gaba da dukiyoyi da kudade masu yawa.

Mutanen da suka ji rauni ana musu magani a babbar asibitin Tangaza.

A cewar kakakin hukumar, wani dattijo wanda ya zo kasuwa don sayen abubuwa ya rasa ransa sakamakon wannan rikicin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel