Nigerian news All categories All tags
Sun auri juna bayan kwanaki shida da gamuwa a dandalin sada zumunta

Sun auri juna bayan kwanaki shida da gamuwa a dandalin sada zumunta

Bayan kwanaki shida da yin gamo a dandalin sada zumunta na facebook, Chidinma Amedu ya zamto angon Sophy Ijeoma, inda aka daura musu aure a ranar 6 ga watan janairun 2018.

Wannan lamari na al'ajabi da ban mamaki ya faru bayan da Chidimma ya watsa wata sanarwa tun a ranar 31 ga watan Dasumbar 2017 a shafinsa na sada zumunta da cewar yana neman wadda ke sha'awar aurensa.

Watsa wannan sanarwa ke da wuya mata da dama suka rinka aika sakonninsu na bayyana sha'awar aurensa, inda amaryarsa Sofie tana daya daga cikinsu.

Sai dai Sofie ta bayyana cewa, a fari tayi tunanin zolaye itama sai ta aika da sakon cikin zolaya na nuna amincewa da bukatar Chidimma ashe Mai Duka ya kaddara.

Sofie da Chidimma

Sofie da Chidimma

Daga wannan lokaci Chidimma yayi tattaki daga birnin Abuja har zuwa jihar Enugu domin saduwa da Sofie, inda yayi nasarar ganawa da ita da kuma ta karbe shi hannu biyu-biyu.

KARANTA KUMA: Ya kamata Buhari ya saki Dasuki da El-Zakzaky - Udeogaranya

Sofie da Chidimma sun nemi amincewar danginsu domin yana daya daga cikin al'adar kabilar Ibo na sanya albarka akan wanda mutum ya nufaci aura, kuma aka yi sa'a kowane dangi ya amince.

A takaice dai wadannan abokai na dandalin sada zumunta sun zamto abokan zama na dindindin, domin kuwa an daura musu aure a ranar 6 ga watan Janairun shekarar nan kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel