Ashshaaa! Yadda wani Suruki ya halaka matar ɗansa da bindigar toka a jihar Neja

Ashshaaa! Yadda wani Suruki ya halaka matar ɗansa da bindigar toka a jihar Neja

Wani manomi mazauni karamar hukumar Gbako ya shiga matsanancin hali bayan ya bindige surukarsa, matar dansa a bisa kuskure da bindigar toka, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta shaida cewar Umar Wakili ya dirka ma surukarsa tasa, Talatu Muhammed harsashi ne a watan Nuwamba na shekarar 2017, a lokacin daya dawo daga gona yana dauke da bindigar a kafadarsa.

KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Maryam Booth ta taka rawa a cikin Fim din Turanci ‘Sons of the Caliphate’

Hadarin ya faru ne a lokacin da Umar yake kokarin sauke itacen da ya yo daga gona, a sa’annan ne bindigar ta tashi, har harsashin ya bigi Talatu a kirjinta, nan take ta fadi matacciya.

Dansanda mai kara, Sajan Mohammed Ilimi ya shaida ma Kotu cewar wannan laifi ya saba da sashi an 221 na kundin hukunta manyan laifuka, sa’annan ya bukaci a dage sauraron karar har sai sun kammala gudanar da binciken lamarin.

Bayan sauraron karar, sai Alkali Hamza Muazu ya dage sauraron karar zuwa 7 ga watan Maris don cigaba da sauraron karar, sa’annan ya bukaci a garkame masa wanda ake tuhumar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng