Hotunan Attahiru Bafarawa tare da ɗansa yayin da suka shiga Ka’aba
Bukatar maje Hajji Sallah, sai dai idan mahajjata zasu samu damar shiga Ka’abah, lallai da sai sun shiga, domin kuwa ba karamin daraja bane, haka zalika waje ne da Allah ke amsar addu’o’in bayinsa.
A iya cewa wani tsohon gwamnan Najeriya da iyalinsa sun samu tagomashi, bayan da masarautar kasar Saudiyya ta basu damar shiga dakin Allah, Ka’abah da nufin gudanar da ibada.
KU KARANTA: Yaron Atiku yayi watsi da hukuncin Kotu, ya ƙwace Ɗansa daga hannun Uwarsa
Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa ne ya samu wannan dama tare da dansa Abubakar Bafarawa, kamar yadda wani ma’abocin kafar sadarwar zamani, Nuhu Aminu Dalhati ya sanar.
Legit.ng ta kalato ba wannan bane karo na farko da dan Najeriya ke shiga Ka’aba ba ba, tunda ko a baya ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu shiga yayin wani aikin Umarah da ya je.
Sauran wadanda suka taba shiga Ka’aba daga Najeriya, akwai Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardauna, tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Sani da sauransu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng