Wani saurayi ya yi karar bazawara da mahaifinta bayan sun ci kudinsa sun hana shi aurenta

Wani saurayi ya yi karar bazawara da mahaifinta bayan sun ci kudinsa sun hana shi aurenta

- Wani mutum ya maka wata bazawara da mahaifinta a kotu bayan sun amshe masa kudi kuma sun hana shi aurenta

- Yace sun karbi kudin aure a wurinsa har N710,000

- An bayar da belin budurwar da mahaifinta a kan kudi N500,000

Wani dattijo, Inusa Aliyu, da 'yar sa, Jamila, sun gurfana a gaban wata kotu a jihar Nasarawa bisa zarginsu da zamba cikin aminci ga wani masoyin Jamila.

Ana tuhumar su da aikata laifuka uku da suka hada da cin amana, Cuta, da zamba cikin aminci.

Dan sanda mai gabatar da kara, Frank Swem, ya shaidawa kotu cewar wani mutum, Yusuf Mamuda, ne ya shigar da korafi ofisoshinsu dake Masaka yana mai zargin wani mutum, Haruna, da hada baki da mahaifin Jamila tare da damfarar sa kudi N650,000 da sunan za'a ba shi auren ita Jamila.

Wani saurayi ya yi karar bazawara da mahaifinta bayan sun ci kudinsa sun hana shi aurenta
Wani saurayi ya yi karar bazawara da mahaifinta bayan sun ci kudinsa sun hana shi aurenta

Ya kara da cewa sun karbi kudin ne da sunan kyautar aurenta.

Mamuda ya ce, Haruna da mahaifin bazawarar sun yi amfani da aure ne sun zambace shi saboda sun san yana neman matar da zai aura..

"Asirin su ya tonu ne bayan na fara bincike domin gudun yin aure a cikin aure tunda Jamila bazawara ce, na bukaci a bani shaidar mutuwar aurenta amma sai suka fara yi min wasa hankali kafin daga bisani su bukaci na bayar da N60,000 domin su je Zamfara su kawo min shaidar," a cewar Mamuda.

DUBA WANNAN: Akwai dalilin da ya saka ni auren mata uku lokaci guda

Dan sanda mai gabatar da kara ya kara shaidawa kotu cewar Mamuda ya basu adadin kudin da suka bukata amma duk da haka sun gaza kawo masa shaidar mutuwar auren Jamila kafin daga bisani ita, Jamila, da kanta ta fada masa cewar tun farko ba ta da niyyar aurensa kuma da bakinta ta fada masa cewar duk abinda ya faru hadin baki ne tsakanin mahaifinta da Haruna domin kawai su damfare shi.

Wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin da ake tuhumar su da aikatawa.

Alkalin kotun, Yakubu Ishaku, ya amince da bayar da su beli a kan kudi N500,000 kowanne mutum tare da wani na kusa da su da zai tsaya masu, kazalika ya daga sauraron karar ya zuwa ranar 19 ga wata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng