Yaron Atiku yayi watsi da hukuncin Kotu, ya ƙwace Ɗansa daga hannun Uwarsa

Yaron Atiku yayi watsi da hukuncin Kotu, ya ƙwace Ɗansa daga hannun Uwarsa

Duk da hukuncin wata Kotun Majistri inda ta mika mallakin yayan tsohon mataimakin tsohon shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ga tsohuwar matarsa, Yaron ya yi kotu karan tsaye.

Wannan lamari ya faru ne bayan kammala shari’ar a Kotun Majistri dake unguwar Tinubu, jim kadan bayan Alkali Kikelomo Ayeye ya mallaka ma Fatima Bolori yayansu Amir da Amira, biyo bayan rabuwar aurensu, amma Aminu yayi kunnen uwar shegu da hukuncin, duk da cewa bai halarci zaman kotun ba.

KU KARANTA: Sojojin sun kama wani sojan gona yayin da yake cin zalin jama’a a Legas (Hotuna)

Jaridar The Nation ta ruwaito Aminu ya tari Fatima ne, inda ya wufce dansu namiji, Amir daga hannunta, sa’annan ya jefa cikin motarsa, kuma ya kulle, nan da nan yayi wuf ya tsere da shi.

Yaron Atiku yayi watsi da hukuncin Kotu, ya ƙwace Ɗanda daga hannun Uwarsa
Yaron Atiku da Iyalinsa

Kafin nan, Alkali Kikelomo ya karanto hukuncin Kotun ga masu shari’ar, inda ya umarci Aminu ya dinga biyan Fatima naira 250,000 a duk wata don kulawa da lafiyar yaran, iliminsu da kuma walwalarsu, amma ta bashi daman zuwa yana ganinsu lokaci zuwa lokaci.

“Biyo bayan rashin halartar wanda ake kara da lauyoyinsa, don haka na mallaka ma Ummi Fatima Bolori rikon yayansu, Amir da Amira, kuma za ta rike su a gidansu dake unguwar Katampe dake garin Abuja.

“Kotu ta baiwa wanda ake kara damar ziyartar yayan nasa, kuma zai iya neman izinin su yi hutu a wajensa, amma sai ya dinga biyansu kudi N250,000 duk wata don kulawa da yaran.”Inji Alkali.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a shekarar 2007 ne dai Aminu ya auri Fatima, sai dai auren ya mutu a shekarar 2011.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng