Kungiyar PCN da hadin gwiwar Jami’an tsaro sun kama babban dilan codein a Nasarawa
- Babban dilan Codein a jihar Nasarwa ya shiga hanun hukuma
- shugaban kungiyar PCN ya ce an kama Amaechi Okoronkwo da kwalaben codein 66o
- Tun shekara 2015 jami'an tsaro suke neman Amaechi Okoronkwo ruwa a jallo inji shugaban kugiyar PCN
Kungiyar masu sayar da maguguna (PCN) da hadin gwiwar jami'an yaki da miyagun kwayoyi (NDLEA) da jami’an hukumar SSS sun kama wani baban dilan codein a jihar Nasrawa a ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu.
Shugaban hukumar PCN, Mista Okpalaeke Nwora, ya shaidawa wa manema labaru a aukuwan wannan lamari ranar Alhamis.
Mista Okpalaeke Nwora, yace hadin gwiwa tsakanin kungiyar PCN da jami’an tsaro yasa aka samu nasarar kama babban dilan codein na jihar Nsarawa, Amaechi Okoronkwo da mataimakin sa, Frederick Uchenna a wata shago dake kan hanyar UAC a lafiya.
Nwora ya ce, tun a shekara 2015 jami’an tsaro suke neman, Amaechi, ruwa a jallo kafin suka samu nasara kama shi a Lafiya da kwalaben codien 660 wanda farashin su ya kai kimanin N700,00.
KU KARANTA : Yansada sun gano sabuwar sansanin fataucin dan Adam a jihar Legas da ceto yara shida
Nwora yace, binciken da aka yi ya nuna duka codein din da aka shigo da su Nasarawa daga Onitsha aka kawo su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng