Sanata ya bayyana yadda rikicin makiyaya da manoma zai kawo barazana ga tsaron abinci

Sanata ya bayyana yadda rikicin makiyaya da manoma zai kawo barazana ga tsaron abinci

- Sanata Suleiman Adokwe yayi Allah wadai da hare-hare da yan bindiga ke kai wa yan Najeriya, musamman yan karkara

- Dan majalisan na jihar Nasarawa ya yi kira da a dauki matakai cikin gaggawa da ingantacciyar hadin kai don kawo karshen rigingimu tsakanin manoma da makiyaya

- Adokwe, wanda ya kasance shugaban kwamitin labarai da al’adu, yace hadin kan zai taimaka wajen magance sauran al’amura

Sanata Suleiman Adokwe (PDP kudancin Nasarawa) ya yi kira da a dauki matakai cikin gaggawa don kawo karshen rigingimu da manoma da makiyaya ke ci gaba da yi don guje ma mumunar sakamako “musamman karewar kayan abinci”.

Adokwe ya fadi hakane a ranar Laraba, a lokacinda ya ziyarci wadanda al’amarin ya shafa a Nasarawa da Benue.

Adokwe, shugaban kwamitin Labarai da al’adu, wanda ya kai kayan agaji fadar sarkin Awe, yayi kira ga hadin kai don tsayar da rikicin.

Ya bayyana cewa hadin kan ne zai taimaka ma masu ruwa da tsaki wajen magance damuwa kamar talauci, yunwa, rashin aiki da sauran al’amura da suka kasance sanadiyan tashe tashen hankalin.

Sanata ya bayyana yadda rikicin makiyaya da manoma zai kawo barazana ga tsaron abinci
Sanata ya bayyana yadda rikicin makiyaya da manoma zai kawo barazana ga tsaron abinci

Yayi nuni cewa babu al’umma dake iya rayuwa cikin tarzoma, ya kuma bukaci kungiyoyi da su rungumi tattaunawa da kuma kokarin fahimtar juna da daraja.

Adokwe ya tabbatar ma basaraken cigabarsa da goyon baya ga kokarinsa na tabbatar da tsayayyar jihar Nasarawa, ya kuma bukace shi da ya kai kuka zuwa ga masu ruwa da tsaki don kowa ya kasance tare da munufar gina zaman lafiya.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu ban ga matana hudu da yara 18 ba – Wanda harin makiyaya ya cika da shi

Ya shawarci yan sansanin gudun hijira da su kasance masu hakuri, masu bin doka kuma su guji tsotsayin keta doka.

A martaninsa, Alhaji Abubakar Umar, sarkin Awe, ya yabi dan majalisan kan karimcinsa, ya kuma bukace shi da ya mai sadarwa tare da gwamnati don karfafa harkar tsaro a yankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng