Hukumar EFCC ta bukaci kotu ta mallaka mata gidan Ikoyi
- Hukumar EFCC ta bukaci kotu ta mallaka mata gidan Ikoyi da aka boye makudan kudade
- Lauyan EFCC ya ce kotu ta malaka ma hukmar EFCC gidan Ikoyi saboda zamban da akayi kafin aka saya gidan
Alkali babban kotun tarayyya na jihar Legas, Jastis, Saliu Saidu, ya sanar da ranar 19 ga watan Janairu, 2018 a matsayin ranar da zai zartar da hukunci akan gidan Ikoyi dake jihar Legas
Hukumar EFCC ta ce, matar tsohon shugaban hukumar NIA, Folashade Oke, ta mallaki gidan Ikoyi da aka boye dala miliyan $43.3m, da naira miliyan N23m.
Hukumar ta gano, Folashade Oke, ta biya $1.6m a lokacin da ta saya gidan a tsakanin watan Agusta zuwa Satumba na shekara 2015.
Lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo ya bukaci kotu ta mallaka wa hukumar EFCC gidan Ikoyi saboda irin zamba da aka yi kafin aka saya gidan.
KU KARANTA : 'Yan gudun hijira sun ki karban kudin hawa mota da gwamnati ta raba mu su
Kwanakin baya Union Bank Plc, ta bukaci kotun ta mallaka mata gidan saboda kwastoman ta ya saya gidan da sunan ta.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng