Baƙin haure 200 sun dilmeyi yayin ketare tekun bahar Maliya
Rahotanni da sanadin jaridar Premium Times sun bayyana cewa, wani jirgin ruwa ya dilmeye dauke da bakin haure 200 'yan kasar Najeriya da wasu kasashen a yayin ketare tekun bahar Maliya akan hanyarsu ta zuwa kasar Italiya da kuma Andalus.
Kungiyar haure ta duniya wato IOM ita ta bayyana hakan da sanadin kakinta na reshen Libya, Christine Petre, inda tace bakin hauren sun bar gabar Azzawiyah da Al Khums ta kasar Libya.
Legit.ng ta fahimci cewa, mafi akasarin wadanda suka tsallake rijiya da baya sun hadar da 'yan kasashen Senegal, Mali, Najeriya, Bangladesh da kuma Pakistan.
KARANTA KUMA: Rayuka takwas sun salwanta a wani hatsarin jihar Kano
A rahoton kungiyar IOM, an nemi kimanin mutane 100 an rasa yayin da 200 da aka tabbatar suka rasa rayukansu a binciken da aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata.
Majalisar dinkin duniya ta ce za ta ci gaba da tallafawa bakin haure wajen bayar da agaji ga wadanda ibtila'i makamancin wannan ya afkawa.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng