Majalisar wakilai ta shiga maganar hana wata lauya saka hijabi
- Majalisar wakilai ta shiga batun nan mai sarkakiya na hana wata lauya saka hijabi
- Batun nuna wariya ga lauyan saboda saka hijabi ya jawo cece-kuce a Najeriya
- Ana saka ran za'a yiwa dokar hana saka hijabin kwaskwarima
Majalisar wakilai ta yunkura domin kawo karshen batun nan na nuna wariya ga wata lauya, Furdaus Amosa, da ya jawo cece-kuce da muhawara tsakanin mabiya mabanbantan addinai a Najeriya.
Majalisar ta shiga maganar ne biyo bayan wani dan majalisar daga jihar Kano, Honarabul Abubakar Danburan, ya jawo hankalin majalisar bisa yadda batun saka hijabin ya jawo nuna yatsa tsakanin mabiya addinan Islama da Kirista da kuma yadda lamarin ya jawo hankalin kafafen yada labarai na duniya.
Da yake gabatar da kudirin, Danburam, ya ce Furdaus, wacce ta kammala karatun lauya a jami'ar Ilorin dake jihar Kwara, ta cancanci samun shaidar zama lauya mai kwarewa duk da an ki bata shaidar hakan saboda saka hijabi ranar bayar da takardan shaida. Ya kara da cewa abinda Furdaus ta yi bai sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya ba.
Makarantar horar da lauya ta kasa taki amincewa ta mika shaidar nasarar samun horon aikin lauya ga Furdaus saboda kawai ta saka hijabi a ranar, Talata, 12 ga watan Disamba, 2017. Hukumomin makarantar bayar da horon sun ce saka hijabin ya sabawa dokokinsu.
DUBA WANNAN: Iran ta haramta koyar da turanci a makarantun firamaren kasar
Tuni dai shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa da sarkin musulmi suka dora alamar tambaya a kan wannan doka ta makarantar horan lauya.
Kazalika masu bibiyar lamarin sun ce cece-kuce a kan batun ya jawo hankalin kafafen yada labarai na kasashen ketare irinsu Al-Jazeera da CNN.
Masana harkar lauya sun ce Furdaus ba ta saba wata doka ba, a saboda haka bai kamata a hanata takardar shaidar kammala karbar horon ba, domin ko a kasashen da basu da musulmi da yawa basa nuna kyama ko wariya ga yanayin shigar ala'ada ko addinin dalibansu.
Majalisar ta umarci kwamitinta a kan harkokin shari'a da ya gudanar da bincike a kan wannan dambaruwa domin bawa majalisar shawara a kan matakin da ya kamata ta dauka.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng