Har yanzu ban ga matana hudu da yara 18 ba – Wanda harin makiyaya ya cika da shi

Har yanzu ban ga matana hudu da yara 18 ba – Wanda harin makiyaya ya cika da shi

- Wani wanda ake zargin harin makiyayan ya shafa yayi kukan bacewar iyalansa a hari da aka kai jihar Benue kwanan nan

- Akpenheen Amile, yace matansa hudu da yara 18 sun bace tun lokacin da aka kai hari kan wasu kauyuka a kananan hukumomin Guma da Logo

- Amile wanda ya kasance mai gadin dabbobi ya samu rauni daga harin

Akpenheen Amile, wanda ya kasance dan banga, ya samu rauni sakamakon alburusai da aka harba a harin ranar 2 ga watan Janairu kan kauyen Guma, jihar Benue, yace har yanzu bai iya gano inda matansa hudu da yara 18 suke ba.

Amile ya bayyana ma kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Laraba a Makurdi cewa, “Ina cikin zafin alburusai da suka mun rauni, amman bana jin zafin kamar zafin rashin gane wani irin hali matayena da yarana suke ciki.”

Kamfanin Dillancin Labarai ta rahoto cewa kauyuka biyar a yankunan Guram da Logo ne yan bindiga suka kai hari a ranar 1 da 2 ga watan Janairu.

A cewar hukuma dake bayar da agaji na jihar Benue (SEMA), akalla mutane 73 ne yan bindigan suka hallaka.

Har yanzu ban ga matana hudu da yara 18 ba – Wanda harin makiyaya ya cika da shi
Har yanzu ban ga matana hudu da yara 18 ba – Wanda harin makiyaya ya cika da shi

Amile, mai mata biyar, ya bayyana cewa matarshi ta biyar ce kadai ta kasance tare da shi, dan bangan wanda ke samun kulawa a asibitin koyarwa na jihar Benue (BSUTH), yace an habe shi ne a dayan kafanshi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rundunar yan sanda ta tura jami’anta 8,000 kan zanga-zanga kungiyar kwadago a Kaduna

Amile, yayi ikirarin cewa yan bindigan sun kasance da shigeairin na makiyaya, yace sun iso misalin karfe 5 na yamma inda suka soma harbi jama'a.

Yayinda yake magana da mai fassara, Amile ya bayyana cewa ya kasance tare da sauran yan banga wadanda gwamnatin jihar Benue ta kwasa aiki don aiwatar da dokar hana kiwo, a lokacinda yan bindigan suka kai masu hari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng