Gwamnatin Kaduna ta samu izinin kama yan kungiyar kwadago dake zanga-zanga
- Gwamnatin jihar Kaduna ta samu izinin kama masu zanga-zangan tashin hankali a jihar
- Gwamnatin tace zata kama duk dan kungiyan kwadago (NLC) da kungiyar malamai (NUT) da ya daukaka zanga-zangan tashin hankali
- Gwamnatin ta zargi kungiyoyin biyu da rusa majalisar dokokin jihar a lokacin zanga-zanga
Gwamnatin jihar Kaduna ta bada sanarwa a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu, cewa ta samu izinin kama mambobin kungiyar Kwadago (NLC) da kungiyar malamai (NUT) masu zanga-zangan tashin hankali a jihar.
Gwamnatin ta zargi kungiyoyin biyu da zanga-zangar tashin hankali kan sallamar malamai da ikirarin cewa a lokacin zanga-zangan kwanan nan, mambobin kungiyar kwadago (NLC) da na malamai (NUT) sun kai hari inda suka yi rushe rushen majalisar dokokin jihar.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa mai magana da yawun Gwamna Nasir El-Rufai, Samuel Aruwan, ya bayyana haka ne a wani jawabi ga manema labarai a jihar.
KU KARANTA KUMA: El Rufa'i na neman amfani da 'Yan sanda wajen gurgunta yajin aikin malamai – Kungiyar kwadago
Duk da haka, Aruwan yace iyaye sun nuna goyon baya ga gwamnatin jihar bisa shawara da ta yanke na sallamar malamai wadanda basu cancanta ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng