Yansada sun gano sabuwar sansanin fataucin dan Adam a jihar Legas da ceto yara shida
- Rundunar yansadar jihar Legas sun kama wata yarinya mai shekaru 25 da ta mallaki sansanin fataucin dan Adam a Legas
- Kwamishinan yansadar Jihar Legas ya ce ana sayar da yaran dake sanin da comfort ta gina kamar bayi
- Comfort Anwana ta ce yaran yan uwanta ke karkashin kulawanta
Rundunar yansandar jihar Legas sun ceto yara shida masu shekaru tsakanin uku zuwa 10 a wani sansanin masu fataucin dan Adam da suka gano a unguwar Ejigbo dake Legas.
Rundunar yansadar jihar Legas sun kama mai sansanin, Comfort Anwana, mai shekaru 25 a lokacin da suka kaiwa wurin sammame a ranar Talata.
An kama yan uwanta, Gift mai shekaru 28, da Blessing, mai shekaru 23 da suke zama tare da ita a sansanin.
Dukan mata haifaffun jihar Akwa Ibom ne daga karamar hukumar Oron.
KU KARANTA : CJN ya gargadi lauyoyi akan furta kalaman batanci
Kwamishinan yansadan jihar Legas, Edgal Imohimi, wanda ya jagoranci rundunar da suka kai wai wurin sammame yace sansanin ba gidan kula da marayu bane.
Yace suna sayar da yaran kamar bayi a gidan, kuma ana tura su aiki a gidajen mutane. Kwamishian ya ce za su yi bincike su gano yadda yaran suke shiga hanun Comfort.
Comfort Awana, ta fadawa manema labarai cewa yaran dake karkashin kulawanta yan uwanta ne wanda babanin su suka mutu.
Ta ce tana taimakon iyaye su mata kula da yaran su, kuma suna zuwa duba su lokaci lokaci.
“Daya daga cikin yaran sansanin mai suna, Lawrence, yace bai san sunan mahaifin sa ba. Mahaifiyar ta kawo sa gidan kuma tana zuwa duba shi lokaci zuwa lokaci amma ba san irin sana’ar ta ke yi ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng