Gwamna ya tsorata da hare haren Fulani, ya tattaro ƙauraye da ýan taurin jiharsa don bashi tsaro

Gwamna ya tsorata da hare haren Fulani, ya tattaro ƙauraye da ýan taurin jiharsa don bashi tsaro

A sakamakon cigaba da ta’azzarar hare hare tsakanin Fulani makiyaya da manoma, gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya tattaro yan tauri, matsafa da kuma kaurayen jihar don su tsare al’ummar jihar.

Gwamnan ya bayyana musu cewar su dage wajen bayar da tsaro a jihar, musamman don bashi da wani da zai taimaka ma jihar a Abuja, amma ya ja kunnensu da kada su dauki hukunci a hannunsu.

KU KARANTA: Aiki ga mai ƙare ka: Babban sufetan Yansandan Najeriya ya isa jihar Benuwe kan lamarin tsaro

Fayose ya bayyana haka ne yayin dayake ganawa da mafarautan da suka fito daga kananan hukumomin jihar guda 16, inda yake fada musu kowa yayi amfani da tsafe tsafensa don kare jama’ansu daga hare haren Fulani.

Gwamna ya tsorata da hare haren Fulani, ya tattaro ƙauraye da ýan taurin jiharsa don bashi tsaro
Gwamna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamna Fayose yana cewa “Na samu labarin wasu Fulani makiyaya masu suna ‘Bororo’ sun fara shiga gandun dazukan jihar Ekiti, don haka nake bayyana ma gwamnatin tarayya cewar Fulani sun shigo don su kashe mu.

Gwamna ya tsorata da hare haren Fulani, ya tattaro ƙauraye da ýan taurin jiharsa don bashi tsaro
Gwamna

“Kada ku bari wani ya shigo jihar nan da sunan kiwon dabbobi da zarar karfe 8 na dare ya wuce, sa’annan ku tabbatar kun caje duk wani mai shigowa jihar nan. don haka kowa ya bude idanunsa.” Inji Gwamna.

Gwamna ya tsorata da hare haren Fulani, ya tattaro ƙauraye da ýan taurin jiharsa don bashi tsaro
Gwamna

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: