Hotunan sabbin jiragen kasa da ake daf da kaddamarwa domin sufuri iya birnin Abuja
- Gwamnati na daf da kaddamar da wasu sabbin jiragen kasa
- Jiragen zasu ke sufuri ne iya kwaryar birnin Abuja
- Shirye-shirye sun yi nisa
Gwamnatin tarayya na daf da kaddamar da wasu jiragen kasa na zamani da zasu ke jigilar mutane iya kwaryar birnin Abuja.
Shirye-shirye tuni sunyi nisa kamar yadda zaku iya gani cikin hotunan da muka kawo maku.
Mun ci karo da hotunan ne a shafin tuwita na mai bawa shugaban kasa shawara a bangaren kafafen watsa labarai na zamani (New media), Bashir Ahmad, inda yake nuni da cewar daf ake da fara more wannan sabon cigaba a bangaren sufuri.
A ranar Alhamis da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da karin wasu sabbin jiragen kasa guda goma da zasu ke jigilar mutane daga Abuja zuwa Kaduna. Kuma ko a lokacin da shugaban ya kaddamar da sabbin jiragen saida ya jaddada cewar zai game dukkan biranen Najeriya da titin jirgin kasa domin inganta harkokin sufuri.
DUBA WANNAN: Hukumar raya birnin Abuja za ta rushe wasu gine-gine 750
Sabbin jiragen da za'a kaddamar a birnin na Abuja, ba sune irinsu na farko ba a Najeriya, domin tuni jihar Legas ta kaddamar da irinsu.
Babu wani jawabi daga ministan sufuri, Rotimi Amaechi, dangane da batun sabbin jiragen na Abuja, kazalika babu wani rahoto a kan ko gwamnatin tarayya ce ko ta jiha keda alhakin aikin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng