Aiki ga mai ƙare ka: Babban sufetan Yansandan Najeriya ya isa jihar Benuwe kan lamarin tsaro
Biyo bayan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari ga babban sufetan Yansandan Najeriya nay a tattara inasa inasa ya koma jihar Benuwe sakamakon tabarbarewa tsaro a jihar, Sufetan ya a cika umarni.
A yau laraba 9 ga watan Janairu ne babban sufetan, Ibrahim Idris ya isa jihar Benuwe a wani yunkuri na magance rigingimun dake tsakakin Fulani makiyaya da yan kauyukan jihar.
KU KARANTA: Ilimi na cikin mawuyacin hali a Zamfara: Dalibai 24 kacal suka samu nasara a jarabawar NECO
Legit.ng ta ruwaito sufetan ya isa jihar dauke da sabbin tsare tsare da kum dabaru irin na tsaro don tabbatar da zaman lafiya, doka da ka’ida, tare da dakatar da hare haren da a yanzu ya janyo asarar rayuka da dama a jihar.
Kafin tafiyarsa jihar, IG Idris ya gana da ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau tare da ministan noma da kuma gwamnonin jihohin da rikicin makiyaya da manoma ya shafa.
Dayake bayani ga mahalarta taron, minista Audu Ogbeh ya bayyana cewar gwamnatin ta dauki matakin gina gandun dabbobi na ekta 5,000, don amfanin makiyaya da dabbobinsu, inda yace nan bada dadewa ba za’a fara zartar da wannan mataki.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng