CJN ya gargadi lauyoyi akan furta kalaman batanci
- Shugaban alkalan Najeriyaya bayyana damuwar sa akan yadda ake furta kalaman batanci game da rikicin kujerar senatan Anambara na tsakiya
- Jastis Walter Onnoghen ya gargadi lauyoyin da al’ummar Najeriya akan kalaman batanci
Shugaban alkalan Najeriya CJN, Jastis Walter Onnoghen, ya gargadi lauyoyin da al’ummar Najeriya akan kalaman batanci game da matsalar dake gaban kotu dan yin sharia.
Jastis Walter Onnoghen, yayi wannan jawabin ne ta mai magana da yawu bakin sa, Mista Awassam Bassey, inda ya bayyana damuwar sa akan yadda ake furta kalaman batanci game da rikicin da ya shafi kujerar senatan Anambara na tsakiya dake gaban kotu.
Walter Onnoghen, ya ce kotu za ta daure duk wanda aka kama yana yadda kalaman batanci game da siyasar Anamabara saboda har yanzu kotu ba ta kammala sharia ba.
KU KARANTA : APC ta gayyaci PDP muhawara akan zargin almubazzaranci da naira N400bn
Ya kuma ja hankalin alkalai da kada su kuskura su dauki al’amarin da wasa wajen hukunta duk wandaaka kama da lafin furta kalaman batanci.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng