Jam’iyyar APC reshen kudu maso gabas ta tsayar da Buhari a matsayin dan takaran ta a zaben 2019
-APC reshen Kudu maso gabas ta yanke shawarar tsaya da shugaba Buhari a zaben 2019
- Jiga-jigan APC reshen Kudu maso gabas sun tsayar da Buhari a matsayin takaran su
- Jam'iyyar tayi wannan ne saboda nasarorin da gwamnatin sa ta samu a fanoni daban-daban
Jam’iyyar APC reshen Kudu maso gabas ta tsayar da shugaban kasa Muhamadu Buhari a mastayin dan takaran ta a zaben 2019.
Jam’iyyar ta tsayar Buhari ne a taron da jigajigan jam’iyyar APC na yankin suka gudanar a garin su Ministan Kimiya da fasaha, Dakta Ogbonnaya Onu, Uburu a ranar Talata.
Legit.ng ta samu rahoton cewa duka jiga-jigan APC na yankin Kudu maso gabas suka halarci taron.
Sun yanke shawarar tsayar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a matsayin dan takarar su ne saboda nasarori biyar da gwamnatin sa ta samu a fanoni daban-daban kasar.
KU KARANTA : Majalisar Wakilai ta ki amincewa da kudirin NNPC akan biyan kudin tallafin man fetur
A cikin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu akwai, kaddamar ayyukan cigaba a yankin kudu maso gabas, samar wa matasa aikin yi da kuma tallafa mu su.
Sun kuma bayyana farincinkin su akan manyan mukamai da shugaban kasa Muhammadu Buhari yaba mutanen yankin kudu maso gabas a sabbin nade-naden da yayi kwananan.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng