Wasu ma'aikatan hukumar yaki da cin hanci a jihar Kano sun ajiye aiki
- Sabbin ma'aikatan sabuwar hukumar yaki da cin hanci da sauraron korafin jama'a sun ajiye aiki
- Ana zargin sun ajiye aikin ne saboda kankantar albashin ma'aikatar
- Shugaban Hukumar, Muhyi Magaji, yaki cewa komai a kan batun
Wasu sabbin ma'aikatan hukumar yaki da cin hanci da sauraron korafin jama'a a jihar Kano sun ajiye aikinsu saboda rashin kyawun albashi.
Jaridar Daily Trust ta ce wani ma'aikacin hukumar ya tabbatar mata cewar wasu daga cikin sabbin ma'aikatan hukumar 140 sun mika takardar barin aiki sannan wasu da dama na shirin mika nasu takardun barin aikin.
"Suna barin aikin ne saboda rashin kyawun albashi da hukumar mu ke fama da shi. Ya kamata gwamnati ta yi wani abu a kan hakan kafin duk ma'aikatanmu masu kwazo su gudu sun bar hukumar," inji ma'aikacin hukumar.
DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin binciken badakalar wawure kudin maniyyata aikin Hajji
Ya kara da cewa "Gwamnati ta kashe makudan kudi wajen horar da jami'an hukumar a hukumar EFCC, amma abin takaici ga shi yanzu sai barin aikin suke yi. Na san sabbin ma'aikata guda shida da suka mika takardunsu na barin aiki, sannan wasu 12 na shirin mika nasu kwanan nan."
"Shugaban Hukumar, Muhyi Magaji Rimingado, na kokarin ganin gwamnatin jiha ta yi mana karin albashi, idan har karin bai samu ba to gaskiya ma'aikata da dama zasu bar hukumar," a cewar ma'aikacin.
Jaridar Daily Trust ta tuntubi shugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimingado, saidai ya ce baya gari, don haka ba zai iya cewa komai a kan batun ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng