Rayuka takwas sun salwanta a wani hatsarin jihar Kano
Kimanin almajirai takwas ne suka rigamu gidan gaskiya tare da raunatar mutane 11 a sanadiyar wani mummunan hatsarin mota da ya afku a hanyar Gaya zuwa Gujungu dake jihar Kano.
Kwamandan hukumar kula da lafiyar hanya reshen jihar, Mista Angus Obum Ibezim, shine ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai na jaridar Kano Chronicle.
Legit.ng da sanadin jaridar Daily Trust ta fahimci cewa, wadannan almajiran suna kan hanyar su ne ta zuwa babban birnin Minna na jihar Neja, domin laluben karatun Al'Qur'ani mai girma a yayin da ajali yayi halinsa.
Mista Angus yake cewa, almajiarai 23 ne a cikin motar inda hatsarin ya afku a sakamakon rusa gudu da direban motar ke yi wanda ya wuce misali tare da daukar kaya da mutanen da suka wuce ka'ida a cikin motar.
KARANTA KUMA: Hukumar INEC ta fitar da jadawalin zaben 2019
A yayin haka ne kwamandan yake gargadin direbobin mota da su kaurace gudu da kuma daukar kaya da suka wuce ka'ida da dokar kasa ta gindaya.
Tuntube-tuntuben manema labari ya tabbatar da cewa, wadanda abin ya shafa 'yan asalin kauyen Kawari ne dake karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng