Sai mun rungumi gaskiya da nagarta sannan za mu cimma nasara a matsayin kasa - Osinbajo
- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ne babbar matsala da kasar ke fuskanta
- Ya bukaci yan Najeriya da su cigaba da nuna dabi’un kirki da juriya wajen aiki don cigaban kasar
- Osinbajo ya shawarci matasan Najeriya da su rungumi ilimin kawunansu kuma kadda su raina kasuwanci komai kankantarta
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yace akwai bukatar yan Najeriya su rungumi dabi’un kirki da juriyan aiki don ci gaban kasar.
Osinbajo ya bayyana hakane a taron kungiyar matasan yankin kudu maso yamma a Osogbo a ranar Talata, 9 ga watan Janairu.
Mataimakin shugaban kasar, ya lura cewa rashin kirki da kuma rashawa sun kasance manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta, yace da za’a iya magance rashawa, za’a iya warware kashi 70 na matsalolin kasar.
Yace kasar tayi rashin abokan tarayya a kasashen waje saboda rashin kirki da amana. “Duk kasar da bata karfafawa kan kirki ba zata kasance tana faduwa.
"Dabi’un kirki da juriyar aiki sun kasance wajibi ga cigaban kasarmu,“ a cewar shi.
KU KARANTA KUMA: Ranakun wahala sun kusa zuwa karshe – Oyegun ga yan Najeriya
Ya bukaci matasa da su rungumi nagartar juriyar aiki, ilimantar da kansu sannan kuma kadda su raina kasuwanci komai kankantarta domin da sannu ake hawa tudun tsira.
“Ba sai kun nuna yaudara ko halin sata ba don cimma buri a rayuwa amman dole ku kasance shirye don maida kalu balenku zuwa dama a rayuwa,” a shawararshi.
Osinbajo ya bukaci matasa a kasar da su goyi bayan shirin cigaba na tsawon shekaru 25 na yankin da kuma cigaban kasar ga baki daya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng