Mai dokar bacci: Malamin addini ya halaka wata mata ta hanyar tsafe tsafe

Mai dokar bacci: Malamin addini ya halaka wata mata ta hanyar tsafe tsafe

Wani Malamin addinin Kirista, Olakanye Oni ya gurfana gaban wata kotun majistri kan zarginsa da ake yi da kashe wata mata mai shekaru 39 a jihar Ekiti, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta bayyana dansanda mai shigar da kara, Sufeta Jonhson Okunade ya shaida ma alkalin Kotun, Aderopo Adegboye cewar Faston ya aikata wannan danyen aiki ne a ranar 13 ga watan Disambar bara a garin Ado Ekiti, na jihar Ekiti.

KU KARANTA: Buhari ya raba ma Obasanjo, Abdulsalam, Gowon, Jonathan maƙudan miliyoyin Nairori

Dansandan ya cigaba da shaida ma Kotun cewa ana zargin Faston da kisan matar mai ta hanyar da tsafi, sakamakon takaddama dake tsakaninsu, wanda aka tsinceta matacciya, da wasu abubuwa a cikin farjin ta.

A cewar jami’in Dansanda mai shigar da kara, wannan laifi da ake zargi an aikata ya saba ma sashi na 325 na kundin hukunta manyan laifuka, na jihar Ekiti, shekarar 2012.

Bayan sauraron dukkan bangarorin, sai alkali Aderopo Adegboye ya umarci a garkame masa Faston da ake zargin, sa’annan ya dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Janairu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng