Gwamnatin tarayya ta san masu kai muna hari, dole ne a kama su – Inji gwamna

Gwamnatin tarayya ta san masu kai muna hari, dole ne a kama su – Inji gwamna

- Gwamnan Binuwai ya ce gwamnatin tarayya ta san masu kai wa jihar hari

- Gwamnan ya ce abin da ya kamata a yi a halin yanzu shi ne gwamnati ta kama jagorancin Miyeitti Alla, Kauta Hore

- Ortom ya bukaci al’ummarsa su yi hankuri ko da yake al’amarin tana da zafi

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom yayin da yake hira da jaridar Punch, lokacin da aka tambayi shi me ya sa suka dage a kan kama jagorancin Miyeitti Alla, Kauta Hore.

Gwamnan ya bayyana cewa yana tsammanin abin da ya kamata a yi a halin yanzu shi ne gwamnati ta kama Kautal Hore.

Ortom ya ce wadannan mutane ba su ɓoye ra'ayinsu ba saboda sun fito fili sun yi barazanar karya doka. Ya ce, “Idan gwamnatin tarayya ba ta kama su ba, suna gaya mana cewa mu ba ‘yan Najeriya bane kuma zai zama abin baƙin ciki domin alhakin gwamnatin tarayya ne ta bamu kariya da kuma samar mana da tsaro”.

Gwamnatin tarayya ta san masu kai muna hari, dole ne a kama su – Inji gwamna
Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom tare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Ya ci gaba da cewa wadannan mutane an san su, kuma ya gaya wa shugaban kasa al’amarin.

KU KARANTA: Abinda na fadawa gwamna Ortom dangane da hare-haren Fulani a jihar Benuwe yayin ganawar mu - Buhari

“A halin yanzu, sun kai mu gaban kotu. Sun yi maganganu masu yawa, kuma sun yi mana barazana, barazanarsu sun zama gaskiya. Suna zaune a Abuja tare da gwamnatin tarayya don me yasa gwamnatin ba za ta iya yin wani abu ba?”

“Suna jefa mu a cikin rikici, wanda ba daidai ba ne. Mun yi komai don tabbatar da zaman lafiya a wannan jihar. Ina so in tabbatar wa duk wanda ke zaune a jihar Binuwai cewa za mu ci gaba da kare su da kuma samar da tsaro ga rayuka da dukiya”, inji shi.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar cewa, gwamnan ya bukaci al’ummarsa su yi hankuri ko da yake al’amarin tana da zafi.

Ya ce wannan doka ta zama doka a jihar Binuwai kuma babu gudu ba ja baya. Ya bukaci a hukunta wadanda ke rura wutar rikici a jihar, ya ce, “Ina tabbatar muku cewa Binuwai za ta samu zaman lafiya”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng