Dandalin Kannywood: Ko na sake yin aure ba zan dena harkar fim ba - Khadija Mustapha

Dandalin Kannywood: Ko na sake yin aure ba zan dena harkar fim ba - Khadija Mustapha

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Khadija Mustapha ta bayyana cewa tana da burin cigaba da harkar fim ko da tayi aure a nan gaba.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi da wata mujallar dake buga labaran masana'antar fina-finan Hausa inda tace tana da burin cigaba da shiryawa tare kuma da daukar nauyin fina-finai koda ta yi aure.

Dandalin Kannywood: Ko na sake yin aure ba zan dena harkar fim ba - Khadija Mustapha
Dandalin Kannywood: Ko na sake yin aure ba zan dena harkar fim ba - Khadija Mustapha

Legit.ng dai ta samu cewa jarumar ta kuma zayyana yadda ta dade tana sha'awar yin fim tun tana yarinya karama kafin daga bisani ta tsunduma cikin fim din gadan-gadan da kanta.

Tun da farkon tattaunawar dai jarumar ta labarta cewa ita shekarun ta 27 a duniya sannan kuma ta taba yin aure har ma ta haifi 'ya daya kafin auren nata ya mutu.

Haka zalika jarumar ta bayyana fim din 'Matar Hamza' a matsayin wanda yafi kwanta mata a rai saboda yadda ta fita daga Kano zuwa Zamfara domin yin sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng