Yajin aiki: Ku tura yaran ku makaranta, Gwamna El-Rufai ya roki iyaye a Kaduna

Yajin aiki: Ku tura yaran ku makaranta, Gwamna El-Rufai ya roki iyaye a Kaduna

A yayin da malaman Makarantu suka shiga rana ta biyu suna yajin aiki a Kaduna, Gwamnan jihar, Malam Nasir El Rufa'i ya roki iyaye kan su yi watsi da yajin aiki ta hanyar tura yaransu Makarantu.

Gwamnan ya nuna cewa malaman sun shiga yajin aikin ne don gurgunta shirin gwamnati na yin garambawul a harkar ilimi inda ya kara da cewa za a fitar da sakamakon jarrabawar wadanda suka nemi aikin koyarwa su 43,000 sannan za a tace mutane 25,000 da za a dauka aiki daga wannan adadin.

Yajin aiki: Ku tura yaran ku makaranta, Gwamna El-Rufai ya roki iyaye a Kaduna
Yajin aiki: Ku tura yaran ku makaranta, Gwamna El-Rufai ya roki iyaye a Kaduna

Legit.ng ta samu cewa a baya dai gwamnatin jihar kaduna a karkashin jagorancin Gwamna Malam Nasir El-Rufai ta yi barazarar barazanar korar dukkan malamin da bai je aiki ba a ranar Litinin 8 ga watan janairun shekara ta 2018.

Wannan dai ya biyo bayan wata sanarwa da kungiyar malaman makarantar ta jihar ta bayar na kudurin ta na shiga yajin aikin sai baba ta gani a jihar da zai bara daga litinin din.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng