Dandalin Kannywood: Yadda na koyi shan sigari a fim da karfi-da-yaji - Fati Shu'uma

Dandalin Kannywood: Yadda na koyi shan sigari a fim da karfi-da-yaji - Fati Shu'uma

Fitacciyar jarumar Kannywood Fati Shu'uma ta ce duk da ba ta shan sigari ko kayan maye, an sa ta ta sha sigari a wani fim, wanda kuma hakan ya bata matukar wahala.

Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin da take fira da majiyar mu inda ta ce kwata-kwata wasu jama'a suna yi masu gurguwar fahimta a sana'ar ta su inda ake tunanin ko dukkan su haka suke alhali sana'a ce kawai kuma ba da gaske ba.

Dandalin Kannywood: Yadda na koyi shan sigari a fim da karfi-da-yaji - Fati Shu'uma
Dandalin Kannywood: Yadda na koyi shan sigari a fim da karfi-da-yaji - Fati Shu'uma

Legit.ng ta samu dai cewa da take bayani game da dalilin da yasa tafi fitowa a matsayin muguwa a fim sai ta kada baki tace: "Ba wai haka nike ba, sani akeyi don ni na dace da irin role din shi yasa ake kira ni in fito a role din mugunta."

Haka nan jarumar ta bayyana yadda daraktan fim din ta ya sa ta ta koyi shan sigari da tsiya inda ta bayyana cewa: "Na ja kusan sau uku ina kwarewa, gaskiya na sha wahala sosai."

Daga karshe ne kuma sai jarumar ta bayyana cewa tafi son fim din ta na farko mai suna 'Sai na auri Zango'.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng