NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar kammala sakandare na 2017
Hukumar shirya jarrabawar NECO ta kasa ta fitar da sakamakon jarrabawar da aka zana na 2017 Nuwamba/Disamba.
Shugaban Hukumar, Farfesa Charles Uwakwe ya ce sakamakon ya nuna cewa kimanin dalibai 42,429 ne suka zana jarrabawar a tsakanin watannin Nuwamba zuwa Disamba na 2017.
Legit.ng ta samu cewa jadawalin da hukumar dai ta fitar ya nuna cewa mutane 42,429 ne suka lashi lambar yabo a kwasa-kwasai 5 zuwa sama daga cikin mutane 32,917 da suka zauna jarabawar wanda yake nuni da kaso 77.58 cikin dari.
Haka nan kuma jihar da ta fi tabuka abun kirki itace Ogun inda mutane 4,766 suka lashe kwas 5 zuwa sama daga cikin mutane 5,213 da suka zauna jarabawar.
A dayan hannun kuma jihar Zamfara ce tafi takwalci da inda mutane 24 ne kacal suka ci kwas 5 din daga cikin 186 da suka zauna jarabawar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng